Da Dumi Dumi

An ci tarar kocin Arsenal fiye da Naira Miliyan 3

Rahotannin daga Ingila sun ce Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta ci  kocin Arsenal Unai Emery tarar Fam dubu 8 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 768).

Hukumar ta ce ta ci tararsa ce saboda rashin da’ar da ya nuna wajen yin kwallo da robar ruwa har ta samu wani mai goyon bayan kulob din Brighton and Hobe a lokacin da kungiyoyin biyu suke fafatawa a gasar Rukunin Firimiya.  A wasan an tashi ne ci 1 da 1 da hakan ya bata wa kocin rai.

Sai dai rahoton da jaridar UK Sun ta kalato an nuna ba a dage kocin daga tsayawa a kan layi don kula da ’yan kwallonsa a wasanni na gaba ba.  An ci shi tara ne kawai don ya zama gargadi a gare shi.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya