Da Dumi Dumi

An dage dokar rufe wuraren ibada a Cross River

Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba

Gwamnatin Kuros Riba ta sassauta dokar coci-coci da masallatai a jihar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Christian Ita, ya sanyawa hannu aka raba wa manema labarai, gwamnatin ta ce sassaucin zai fara aiki ne ranar Lahadi 24 ga watan Mayu.

Ta kuma umarci wuraren ibadar su tanadi kayan tsaftace hannu, sannan mabiya su yi amfani da amawali su rufe hanci da bakinsu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “kwamitin dake aikin yaki da cutar COVID-19 zai rika zagayawa ya ga ko an aiwatar da dokar.

“Za a hukunta duk wadanda suka taka ta, hukunci mai tsanani”.

ADVERTISEMENT

Sai dai sanarwar ba ta ambaci ko za a yi sallar Idi da ta Juma’a ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya