Da Dumi Dumi

An daina sayar da fim a faifan CD a kasashen waje – Yakubu Mohammed

Yakubu Mohammed
Yakubu Mohammed

Shahararren mawaki kuma jarumi a Masana’antar Kannywood, Yakubu Mohammed ya ce an bar Kannywood a baya wajen fasahar sayar da fina-finan da nuna su.

Yakubu wanda ake yi wa lakabi da Yaks ya bayyana haka ne bayan ya fitar da wata sabuwar waka da ya yi da Ingilishi mai suna Superstar, wadda ya ce “Waka ce da take magana a kan kara kwarin gwiwa. Idan mutum yana so ya yi abu lallai zai iya yi.”

Ya ce lokaci ya yi da mawakan Hausa za su fara waka da harshen da ya fi bazuwa da karbuwa a duniya.

Yakubu ya ce, “Ya kamata wakokinmu da fasaharmu kada su tsaya kawai a kasar Hausa, ya kamata ya zama cewa za ka iya yin na Hausa za ka iya yin na Ingilishi.”

Ya ce ya fara wakoki ne saboda ya lura cewa an bar mawakan Hausa a baya, sabanin takwarorinsu na Kudu.

ADVERTISEMENT

“Yawanci idan abubuwa suka faru a Arewa, duniya ba ta sani, ba ta jinmu saboda da Hausa muke fitowa mu fada, amma abu daya idan ya faru a Kudu sai ka ji duniya ta dauka ana cewa a zo a taimaka.

Mawakanmu na Hausa babu wanda za ki ji an gayyace shi ko Amurka ko wata kasar. Akwai wani bikin mawaka da ake yi duk shekara a Dubai, babu mutumin Arewa kwaya daya da aka dauka. Amma ’yan Kudu da suke dan sirka Yarabanci da Ingilishi ana kiransu,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

Yakubu ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya dade a Masana’antar Kannywood, ya fahimci cewa an baro masana’antar a baya a fannin ci gaba.

“An riga an wuce wani waje, ba mu farga ba har aka yi mana nisa.

Duk duniya yanzu an daina buga fina-finai a faifan CD, sai dai a kalla ta Intanet wato ta manhajar Youtube ko ta wasu mahajojin.

Amma Kannywood ba ta gane haka da wuri ba. Yanzu haka akwai fina-finai sama da 500 da aka yi amma an kasa fitar da su saboda asara za a yi.

“Kasuwanci dai dama shi ne jigo a kowace sana’a, duk yadda ka so abu ba za ka so yau ka yi gobe ma ka yi amma ka yi asara ba,” inji shi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya