✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure mai shiga burtun kama da Yariman Saudiya don ya yi sata

An daure wani mutumin da ya sha yin shigar burtun kama da Yariman Saudiya don ha’intar masu zuba jari da nufin yin rayuwar kasaita, shekaru…

An daure wani mutumin da ya sha yin shigar burtun kama da Yariman Saudiya don ha’intar masu zuba jari da nufin yin rayuwar kasaita, shekaru 18 a gidan yari, sakamakon wata damfarar da ba ta yi nasara ba, inda wanda ya so ya damfarar ya same shi yana cin naman alade, wanda haram ne Musulunci.

Wata kotu a Miami na Amurka ta hukunta Anthony Gignac, mai shekaru 48, sakamakon damfarar fiye da Naira biliyan 2.5, a yayin da yake karyar cewa shi ne “Sarki Bin Khalid Al-saud.”

Ya sayi motar ke ce raini ta Ferrari da agogunan Roled sa’annan ya kama hayan wani gida na gani-a-fada a tsibirin Kudancin Florida, duk dai da wadannan kudaden damfarar.  Sai dai ya amince caje-cajen da aka masa na damfara da kuma shigar burtun jami’in diflomasiya da sauran tuhume-tuhumen da aka masa.

Masu gabatar da kara dai sunce akalla an kama Mista Gignac sau 11 yana shigar burtun yariman Saudiyan.

An haife shi ne a kasar Colombia, said ai wani iyali a Michigan sun dauke shi a zaman da, dan haka ya zama Baamurke.

Sai dai ya fadawa alkalin da ta yanke masa hukuncin cewa yayi na’am shi ya aikata laifukkan, amma da akwai wasu da suke da hannu dumu-dumu a ciki, dan haka lallai ne su ma a gabatar da su gaban shari’ah.