✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano kudan zuma dubu 80 a dakin ma’aurata

Wasu ma’aurata sun razana ganin yadda aka gano cincirindon kudan zuma da suka kai dubu 80 a  bangon dakin kwanansu a lardin Granada, da ke…

Wasu ma’aurata sun razana ganin yadda aka gano cincirindon kudan zuma da suka kai dubu 80 a  bangon dakin kwanansu a lardin Granada, da ke kasar Sipaniya.

Kafafen sadarwa na zamani na kasar Sipaniya sun yi ta yada rahoton ma’auratan a unguwar Pinos Puente, a lardin Granada, wanda suka bukaci wani mai kiwon zuma da ya binciki bangon dakin kwanansu game da sautin da suke yawan ji.

Wadannan ma’auratan sun dade su na jin karar sauti irin na kudan zuma, wanda suka wannan karar ya nada alaka da sautin kudan zuma, wani lokacin ba su iya yin barci da daddare saboda karan sautin da yake damunsu, don haka suka yanke shawarar su nemi taimakon kwararre a fannin kiwon zuma.

Wani mai kiwon zuma mai suna Sergio Guerrero, shi ya taimaka wajen fitar tarin kudajen zuman da suka manne jikin bangon dakin, wanda ya ce akalla kudajen zuman sun kai dubu 80.

Sergio, ya bayyanawa sadarawa ta La Banguardia cewa, “Tarin wannan kudajen zuman sun kai shekara a cikin dakin su na rayuwa, na yi mamakin yadda ma’auratan ke rayuwa daki daya da dubban kudan zuma na tsawan lokaci.”

Mai kiwon zuma ya ce, sarauniya daga cikin kudar zumar ce ke yin kwai dubu 1,400 a duk rana, amma wannan yawan zuman da suka taru na nuna cewa, kudajen zuman sun kai akalla shekara biyu kafin su kai wannan yawan. Duk da yake ya ce, ya fitar da kudajen zuma kamar rabin miliyan daga gidajen jama’a a wannan shekarar kawai, amma kuma ya ce, bai taba ganin irin wadannan tarin zumar ba.

Sergio, ya shawarci jama’a akan  duk kokacin da suka fahimci cewa, akwai zuma a gidajensu da suke rayuwa, su gaggauta kiran masanin kiwon zuma.