Da Dumi Dumi

An gano mutum na uku da cutar Kurona ta kama a Najeriya

Mista Abayomi Akin Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas
Mista Abayomi Akin Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas

An samu tabbacin sake samun mai dauke da cutar Kurona a Najeriya bayan da Gwamnatin Jihar Legas ta ce an samu wata mata da ta dawo daga kasar Ingila a ranar Juma’a wacce take dauke da cutar a jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Mista Akin Abayomi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar a Talata. Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka ta Kasa (CDC), ta tabbatar da cewa matar ta ga duk alamomin cutar tare da ita a cikin kwana 14 da ta kebe kanta daga jama’a.

“Tana karbar magani a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke  Legas,” inji shi.

Ministan Lafiya ya ce wannan sabuwar cutar ita kadai ce ake da ita a halin yanzu a kasar nan domin mutum biyu da suka kamu da cutar a baya sun warke kuma an sallame su.

Ya tabbatar da cewa wannan bullar ba ta da alaka da ta farko da ta bulla wacce wani mutumin Italiya da ya shigo Najeriya ta hanyar jirgin kasar Turkiya da ake alakanta wanda ya kamu na biyu da shi.

ADVERTISEMENT

’Yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta na zamani na sun yi ta kiran gwamnati ta rufe filayen jiragen saman kasar nan saboda kauce wa yada cutar da wadanda suke dauke da ita daga wasu kasashe ka iya kawowa nan Najeriya. Amma sai a shekaranjiya Laraba ce gwamnati ta dauki wani kwakkwaran mataki a kan haka.

Kasancewar Najeriya kasar bakar fata da ta fi yawan jama’a ya sanya ake irin wadannan kiraye-kiraye tun daga lokacin da aka samu bullar cutar ta farko a Najeriya.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya