Da Dumi Dumi

An haifi saniya mai kai biyu da ido hudu da harce biyu

Saniyar da aka haifa da kai biyu da idanu hudu da harce biyu
Saniyar da aka haifa da kai biyu da idanu hudu da harce biyu

Saniyar wani manomi mai suna Bhaskar, ta haifi wata saniya mai abin mamaki da ba a saba gani ba. Saniyar ta haifi ’yarta ce da kai biyu da idanu hudu da baki biyu da gefen kai daya da kunnuwa a wani gidan gona da ke kauyen Paarasalai a Kudancin Indiya.

Haihuwar wannan saniya ya sa, gidan gonar ya zama wani wuri na musamman da ake zuwa don ganin sabuwar halittar.

Manomin ya razana sosai ganin cewa, bai taba ganin irin wannan saniya ba, tun lokacin da saniyar ta haifi ’ya mai kai biyun.

Bhaskar, bai taba tsammanin cewa, saniyarsa za ta haifi irin wannan halitta ba a cikin gonarsa da ke kauyen Paarasalai.

Ya yi matukar mamakin ganin saniyar ta haifi ’ya mai kai biyu a manne da juna.

ADVERTISEMENT

Ita dai wannan halittar saniya, halitta ce da ba a saba gani ba, ta yadda aka haife ta da idanu hudu da kuma baki biyu, sai kuma wani bangarenta da kunnuwa a gefe daya.

Gonar Bhaskar, ta kasance wajen yawaon bude-ido, inda ake samun baki daga makwabtan garuruwan don kawai su ga irin wannan halitta da aka haifa.

’Yar saniyar mai harce biyu, hakan ya sa ba ta iya tsotson nono, sai dai kullum a rika ba ta madara a cikin roba don shayar da ita.

Saniyar da ’yar da aka haifa suna cikin koshin lafiya, amma akwai shakkun dorewar rayuwar ’yar da aka haifa saboda yanayin halittar da aka haife ta.

Ana iya haifar masu irin wannan halittar a cikin jinsin dabbobin da suka hada da macizai da shanu da kifi da kunkuru.

A cikin macizan da ake kamawa don yin kiwo, ana smun wadanda ake haifa da kai biyu.

Mafi yawan dabbobin da ake haifa da nakasa musamman masu kai biyu na fuskantar matsaloli da dama.

“Wani lokacin ana iya samun an haifi halitta da kai biyu sai a samu daya daga ciki ya fi daya kuma yana rinjayar dayan,” kamar yadda wani kwararren likita Dokta John Kleopfer, ya bayyana wa kafar sadarwa ta ABC.

Mun samo wannan labari ne Daga www.mirror.co.uk/news

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya