✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An horar da manoman alkama sababbin dabarun noma

A kokarinta na daukar matakin da ya kamata don bunkasa samar da alkama a kasar nan,  Hukumar Bincike ta Tafkin Chadi ta fara horar da…

A kokarinta na daukar matakin da ya kamata don bunkasa samar da alkama a kasar nan,  Hukumar Bincike ta Tafkin Chadi ta fara horar da manoman kasar nan kan sabbin dabarun noman alkama da  kasar Masar ke amfani da su da ya hada da amfani da injunan yin noma da wadanda ke yin kunya tare da yin shuka a lokaci guda.

Jagoran Shiyya na Hukumar Farfado da Noma, Farfesa Ibrahim Umar Abubakar shi ya bayyana haka lokacin bude taron horarwar Ga manoman rani da ya gudana a Kano.

Farfesa Umar, ya ce za a gwada wa manoman yadda sababbin dabarun noman alkamar suke ta hanyar daukar manoman zuwa wasu gonaki da aka zaba don su ga yadda abin yake a aikace tare da gane wa idanunsu yadda abin yake bayar da sakamako cikin hanzari.

A cewarsa, sababbin dabarun da aka aro daga kasar Masar suna da karfin kara yawan amfanin gona a kan kowace eka fiye da yadda aka saba samu yayin bin hanyoyin da aka saba da su wajen yin noman alkama inda a karshe manomi ke tashi da amfanin gona kalilan. “Wadannan sababbin dabaru sun hada da yin amfani da wani inji da zai fitar wa manomi kunya da yin shuka a lokaci guda, wannan zai magance asarar da ake samu sakamakon yawon da ruwa ke yi a gonar. Muna fata da samun wadannan sababbin dabaru manoman alkama za su fita daga matsalolin da suke samun kansu a duk lokacin noman,” inji shi.

A jawabin Shugaban Manoman Alkama na Kasa, Alhaji Salim Muhammad, ya ce manoman alkama sun dade suna tafka hasara a duk lokacin noma, don haka a cewarsa, yana da tabbacin sababbin dabarun za su taimaka wa manoman yadda za su kara samun amfani kan wanda suke samu a kowace eka.

Shugaban ya yi kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa su tabbatar cewa manoman alkama sun samu duk wani taimako da za a ba su a kan lokaci.