✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari da yin garkuwa da mutum 3 a Dan-Ali jihar Katsina

Wasu gungun mahara da ake zaton barayin shanu da yin garkuwa da mutane sun kai hari a garin Ɗan-Ali da ke cikin karamar Hukumar Ɗanmusa…

Wasu gungun mahara da ake zaton barayin shanu da yin garkuwa da mutane sun kai hari a garin Ɗan-Ali da ke cikin karamar Hukumar Ɗanmusa a Jahar Katsina. Maharan sun shiga cikin garin da misalin 1:30 na daren Talatar yau.

Bayan shigar su garin sun yi ta harbe-harben bindigogi ba ƙaƙƙautawa, sannan suka tunkari gidajen Alhaji Musa da Alhaji Usman ind sun yi awon gaba da mutum uku da kuma kudaɗe da sauran wasu kayayyakin amfani. Kamar yadda rahotonni suka fito daga garin, maharan har suka gama abin da suke babu wani jami’in tsaron da ya leƙo garin balle kawo wani ɗauki. Babu dai asarar rayuka da aka yi a wannan hari, kamar yadda Aminiya ta samu rahoto.

Yawaitar sata tare da garkuwa da mutane da kuma kashe su a wasu lokuta kullum abin sake sabon salo yake a Jahar ta Katsina wanda hakan yasa har shi Gwamnan Jahar Aminu Masari a ranar Juma’ar da ta gabata ya sanyawa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da satar shanu ko garkuwa da mutane.

Kazalika,Sakataren Gwamnatin Jahar kuma Shugaban Kwamitin Tsaro Dokta Mustafa Inuwa, ya zargi Jami’an Sojojin da aka kawo a Jahar don yaƙar waɗannan ƴan ta’adda da gaza yin wani abin azo a gani a duk faɗin wuraren da aka tura.

Dokta Mustafa ya nuna rashin gamsuwar rawar da sojojin ke takawa a wani shirin da ya gabatar a gidan Rediyon Tarayya Abuja wanda kuma aka yaɗa a sauran tashoshin da ke ƙarƙashin gidan rediyon dake sauran jihohi. Zargin da Babban Jami’in rundunar sojojin ta Bataliya ta 17 da ke Jahar ya musanta. Yankin Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa dai na daga cikin wuraren da ke fuskantar waɗannan hare-hare. Har dai zuwa rubuta wannan rahoto babu wani bayanin da ya fito daga ɓangaren jami’an tsaron.