✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kalubalanci gwamnatin Kwankwaso kan dukiyar al’umma

An kalubalanci gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano kan kokarin juyar da dukiyoyin al’ummar jihar tamfar na kungiyar Kwankwasiyya da gwamnatin ta kafu…

An kalubalanci gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano kan kokarin juyar da dukiyoyin al’ummar jihar tamfar na kungiyar Kwankwasiyya da gwamnatin ta kafu a kan ta, yadda take sa sunan kungiyar a kan dukkan  wani aiki da ta yi ko kuma ta karasa.
Wannan kalubale ya fito ne daga bakin wani dan jihar ta Kano da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa  a garin Damaturu, kuma dan jam’iyyar ANPP, Malam Musa Yusuf Kwankwaso tsallaken Diga, cikin karamar Hukumar Madobi a hirar da ya yi da Aminiya.
Malamin ya ce abin takaici ne ganin irin yadda gwamnatin ta Kano da ke lakaba wa kanta Kwankwasiyya take sanya sunan kungiyar a kan dukkan wani aiki da ta aiwatar ko kuma ta tarar gwamnatin da ta shude a karkashin jam’iyyar ANPP ta fara ta bari, ita kuma ta karasa, abin da ya bayyana da, a ganinsa, aiki ne irin na riya.
Malam Musa Kwankwaso ya ci gaba da cewar, “Ai in har shugaba ya san yana ba abu ne don al’umma su yaba tare da sauke nauyin da ke kansa, ba domin riya ba, babu batun sa shaidar cewar na wata kungiya ce ta kashin kansa, kuma ma ai in har don Allah shugaba yake yi, babu batun waige ga harkokin da yake gudanarwa kan abin da ya shafi ayyukan jama’a.
“Kuma ai batun da gwamnatin ke yi cewar wai tana rubuta shaidar ta Kwankwasiyya ne a dukkan ayyukan da take yi don kar in ta shude gwamnatin da za ta gaje ta ta rika fadin su suka yi ayyukan, a ganina, wannan ba dalili ba ne. Haka nan, a fahimtata, duk irin ayyukan da gwamnatin ke cewa ta yi, ai akwai gwamnatocin da suka shude da suka gudanar da ayyuka muhimmai fiye da na ita gwamnatin ta Kwankwasiyya. Alal misali duk wanda ya san gwamnatin marigayi Abdu Bako ya san da cewar irin ayyukan da ta gudanar ba za a kwatanta ta ba da gwamnatin ta Kwankwasiyya, nesa ba kusa ba”.
Kodayake Malam Musa ya yaba da wasu ayyukan da gwamnatin ta Kwankwasiyya ta gudanar, amma kuma, a cewarsa, riyar da ta sa a ciki ce ta bata kudurin da take da shi.
Daga nan sai ya sake kalubalantar gwamna kwankwaso kan yadda ya yi watsi da wani bangare na mazabarsa wato bangaren Kwankwaso tsallaken Diga ta yadda aka maida su kamar su ba ’yan karamar hukumar ta Madobi ba. A cewarsa, ai ko da a ce suna adawa ne, shi shugaba na kowa ne, ba wai na wani bangare daya ba.