✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai garkuwa da yake samun Naira miliyan 200 a wata 6

Hukumar ‘yan sandan Najeriya a jiya ta kama shahararren mai garkuwa da mutane don neman kudin fansa Abubakar Umar, wanda suka ce yana samun sama…

Hukumar ‘yan sandan Najeriya a jiya ta kama shahararren mai garkuwa da mutane don neman kudin fansa Abubakar Umar, wanda suka ce yana samun sama da Naira miliyan 200 a cikin wata shida, daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

‘Yan sandan sun yi nasarar kama Abubakar, tare da wasu mutum 37 da ake zargi da aikata laifukan yin garkuwa da mutane. A cikin su akwai wani mai suna Abubakar Ahmadu, wanda shi ne ya yi garkuwa da shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (UBEC) Dakta Mohammed Mahmood Abubakar da ‘yarsa Yasmin, a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar 29 ga watan Afrilu 2019.

Kakakin rundinar ‘yan sanda na kasa, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda Frank Mba ne ya bayyana hakan a Abuja. Jami’an ‘yan sandan sun kama wadanda ake zargin ne daga ranar 5  ga Yuni zuwa 19 ga watan 2019.

Jami’an ‘yan sandan sun kuma kama bindigogi 33, alburusai masu rai 77 da kuma motoci biyu kirar Volkswagen.