✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai gidan kangararru a Ibadan tare da ceto mutum 259

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani malamin Musulunci Alfa Isma’il Olore, wanda ya mallaki gidan kangararru a birnin Ibadan, inda suka ceto mutum…

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani malamin Musulunci Alfa Isma’il Olore, wanda ya mallaki gidan kangararru a birnin Ibadan, inda suka ceto mutum 259 da ake tsare da su  a gidan. An kama malamin tare da mataimakansa biyar ne a lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Shina Olukolu ya jagoranci jami’ansa zuwa gidan da ke Unguwar Ojo a birnin Ibadan a ranar Litinin da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai bayani Kwamishinan ’Yan sandan ya ce, yanzu aka fara wannan aiki na gano irin wadannan gidaje da ake tsare mutane ba tare da izini ba a jihar.

Ya ce, an mika malamin da mataimakansa biyar da aka kama ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar domin ci gaba da bincikensu. Kwamishinan wanda yake tare da Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Oyo Hajiya Fausat Ajoke Sanni, sun yi wa gida mai bene biyu dirar mikiya ne inda suka jagoranci shiga cikin wasu manyan dakuna da aka cunkusa mutane a ciki. Ya ce, sun yi nasarar ceto mutum 191 daga bangaren maza da mata 34 da kananan yara 10 da marasa lafiya 23 da jariri daya.

Kwamishina Fausat Ajoke Sanni, ta ce wadansu mutane ne suka bayar da labarin sirri da ya kai ga bankado gidan da aka dade ana gallaza wa mutanen da aka tsare da sunan gyara halayensu da sanya su a kan kyakkyawar hanyar rayuwa amma maimakon haka sai aka cunkusa su cikin dakuna a takure babu isasshen abinci yayin da wadansu daga cikinsu suka kamu da cututtuka iri-iri. Ta ce, gwamnatin jihar ce za ta dauki alhakin kula da mutanen da aka ceto.

Aminiya ta gano cewa, Alfa Isma’il Olore ya yi gadon wannan gida da babban masallacin Juma’a daga mahaifinsa ne.  Sai dai ya gaza amsa tambayoyin da Kwamishinan ’Yan sandan ya yi masa sai dai cikin makyarkyata ya ce, “Dukkan mutanen da muka tsare a cikin wannan gida iyayensu ne suka kawo su da kansu daga ciki da wajen Ibadan domin a yi musu maganin cututtukan da suke damunsu na kangara da tabin hankali. Kuma babu wanda muke daurewa da mari ko sarka muna yi musu addu’a ne. Da yawa daga cikinsu miyagun kwayoyi suke sha kafin a kawo su wurinmu.”

A daidai lokacin da Kwamishinan ’Yan sanda Shina Olukolu, ya bayar da umarnin balle kofofin dakunan da ake tsare da mutanen sai mazauna ciki suka fito sanye da wanduna babu riga a jikinsu inda suka rika nuna jin dadinsu kan kubutar da su da mahukuntan suka yi.

Aminiya ta ce, duk da yake babu mari ko sarka a kafafunsu sai dai akwai da yawa daga cikinsu da suka tagayyara ta fannin ramewa da kanzuwa da kwarkwata a jikinsu. A bangaren maza mafi yawancinsu masu shekara 15 zuwa sama ne, yayin da a bangaren mata  akwai masu kananan shekaru. Wata mata da aka taimaka mata wajen saukowa daga matakalar benen gidan an ji cewa haihuwa ta yi da jaririnta a goye. Kimanin shekara 10 da suka wuce ke nan da mahukunta a jihar suka taba kai irin wannan samame a gidan a inda suka kama malamin da ya gina gidan a matsayin makarantar Islamiyya da Masallacin Juma’a tare da kubutar da wadanda ake tsare da su a wancan lokaci. Amma daga baya aka bayar da belinsa inda ya ci gaba da gudanar da ayyukansa kafin ya rasu kuma babban dansa Alfa Isma’il Olore ya gaje shi.