✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama malami mai almajirai 327 maza da mata a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani malami da ke ajiye yara kanana maza da mata a matsayin almajirai. Kwamishinar ci gaban al’umma ta jihar, Hajiya…

Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani malami da ke ajiye yara kanana maza da mata a matsayin almajirai.

Kwamishinar ci gaban al’umma ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta sanar da hakan a zantawarta da manema labarai.

Hajiya Hafsat ta ce malamin mazaunin garin Zariya ne amma dan asalin garin Dakingari a jihar Kebbi kuma sunansa Malam Ali Maikwari.

“Mun kwashe yara 327 a cikin gidan wanda ya mayar a matsayin makarantar kwana.

“Goma sha bakwai daga cikin yaran da muka kwashe mata ne. Mun samu labarin har aurar da yaran yana yi ga mai so.

“Bai dace ka rika cakuda maza da mata wuri guda ba”, inji kwaminar.

Ta kuma kara da cewa, “Wanna ba addini ba ne kuma bai dace ba. Yanzu haka ana ci gaba da bincike akansa”.

Wasu masharhanta dai na ganin hukumomi sun yi sakaci da suka kasa gano wannan “makaranta” sai yanzu.

A watannin baya an kakkama malaman da ke ajiye yara da sunan gyaran tarbiyya a garuruwa daban-daban na Najeriya.