✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da ta saci jaririn wata 4 a Ogun

Wata mata mai suna Falilat Olatunji da ake zargi da satar jariri dan watanni hudu ta shiga komar ‘yan sandan jihar Ogun. Mai magana da…

Wata mata mai suna Falilat Olatunji da ake zargi da satar jariri dan watanni hudu ta shiga komar ‘yan sandan jihar Ogun.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa, matar ta sace jaririn mai suna Ibrahim Bello a unguwar Kajola da ke yankin mil 2 a Abeokuta, a lokacin da mahaifiyarsa ta aje shi a daki ta tafi tsakar gida tana wanke kaya, sai wacce a ke zarginta sadada ta dauke yaron.

Ya ce, wani mutum mai suna Alhaji Abdul Akeem, ne ya shigar da karar a ofishin rundunar ‘yan sandan yankin lamarin da ya sanya suka dukufa har aka kai ga gano matar a yankin Ilewo Orile.

“A binciken da mu kayi mun gano wacce ake zargin na zaune ne a yankin Ayobo a Legas kana ta taba zama a gidan mahaifan jaririn kuma da ita aka yi bikin sunansa, ta shaida mana cewa ta sace shi ne domin ta nuna wa saurayinta shi a matsayin dan da ta haifa domin ta yi masa karyar cewa, tana da ciki, sai tayi niyyar ta nuna wa saurayin nata yaron da nufin ita ta haife shi.” In ji DSP Abimbola Oyeyemi.

Ya ce, tuni aka damkawa iyayen yaron dansu yayin da wacce ake zargin zata fuskanci shari’a, a karshe ya yi kira ga iyayen yara da su dinga lura da kyau domin kare ‘ya’yan su daga hannun bata gari.