✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da ta tura kishiyarta rijiya da jariri a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi nasarar kame wata mace mai suna Hauwa Lawal mai kimanin shekaru 30 da ake zarginta da hallaka kishiyar ta…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi nasarar kame wata mace mai suna Hauwa Lawal mai kimanin shekaru 30 da ake zarginta da hallaka kishiyar ta a kauyen Rurum da ke karamar hukumar Rano a jihar Kano.

Majiyar mu daga Kafanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta shaida cewa, Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna, ya shaida cewa rigima ce ta barke da wacce ake zargin tare da abokiyar zaman aurenta wato kishiyar ta Zuwaira Sani mai shekaru 35, sai wacce ake zargin ta hankade kishiyar nata ta tura ta rijiya a lokacin da take goye da jariri dan wata 18.

Abdullahi, ya ce jami’an rundunar sun yi nasarar ceto yaron da ransa yayin da mahaifiyar aka tabbatar da mutuwar mahaifiyarsa a asibitin Rano, ya ce an kame wacce ake zargin ne da misalin karfe daya na ranar Asabar din da ta gabata bayan ta tsere biyo bayan faruwar lamarin.