✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matasan da ke fasa shago a Jigawa

Rundunar ’yan sanda ta samu nasarar kama wadansu matasa biyu da suka kware wajen fasa shagunan mutane suna yi musu sata.  Haka kuma matasan sun…

Rundunar ’yan sanda ta samu nasarar kama wadansu matasa biyu da suka kware wajen fasa shagunan mutane suna yi musu sata.  Haka kuma matasan sun kware wajen satar babura suna canja musu kamanni suna sayarwa.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa SP Audi Jinjiri ya tabbatar da hakan a lokacin da yake baje kolin matasan ga manema labarai.

Ya ce rundunarsa ta samu nasarar kama matasan biyu ne a lokacin da suke yin sintiri a Dutse inda suka kama Usman Tijjani dan shekara 21 yana kokarin fasa wani shago da ke kan Titin Hakimi a garin Dutse da tsakar dare.

Ya ce an samu Usman da turamen atamfa shida da takalman mata da mayafai uku inda ya tabbatar ya sato su ne a wurare daban-daban.

Usman wanda dan asalin Jihar Kano ne ya ce yana zuwa Jigawa ne don yin sata tare da hadin bakin abokinsa da yake gayyatarsa suna tafka ta’asar.

Nan da nan jami’an ’yan sanda suka yi nasarar kamo Baffa Wada Garu dan shekara 27 inda ya tabbatar suna aikata satar ce tare da Usman.

Baffa ya tabbatar su suka fasa shagon wani Kabiru Muhammad da ke kan titin Hakimi inda suka saci babura biyu suka kai Kiyawa suka sayar a kan Naira dubu 75.

A binciken da ’yan sanda suka yi bayan sun kama Baffa sun sake gano wasu turamen atamfa da shaddodi da yaduka guda 45 da matasan suka sata a shaguna daban-daban.

Kakakin ya ce da zarar sun gama bincike za su tura wadannan matasa gaban alkali don a yanke musu hukunci.