✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Michel Platini a Faransa

Rahoton da jaridar The Uk Mirror ta Ingila ta ruwaito ya ce a ranar Talatar da ta wuce, jami’an ’yan sanda suka yi nasarar kama…

Rahoton da jaridar The Uk Mirror ta Ingila ta ruwaito ya ce a ranar Talatar da ta wuce, jami’an ’yan sanda suka yi nasarar kama tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Michel Platini.

Platini, mai shekara 63 ana tuhumarsa tare da wadansu da laifin yin magudi a wajen ba Katar damar daukar nauyin gasar cin Kofin Duniya a shekarar 2022 al’amarin da ya sa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dage shi har tsawon shekara 6 daga shiga harkokin wasanni a matsayin hukunci.

Sai dai daga baya an rage tsawon shekarun zuwa 4 bayan ya daukaka kara a Kotun Sauraron Kararrakin Wasanni ta Duniya.

Ana zargin Platini da wadansu jami’an Hukumar FIFA ne da laifin hada baki da yin coge wajen ba Katar damar daukar nauyin gasar cin Kofin Duniya a 2022 wanda hakan ya saba wa dokar FIFA.

An kama Platini ne a garin Nantere da ke Yammacin birnin Paris na Faransa lokacin da yake tafiya.

Tun a shekarar 2015 Hukumar FIFA ta dakatar da Platini daga Shugabancin Hukumar UEFA tare da wadansu jiga-jigai a hukumar. Kuma a bana zai kammala wa’adin dagewar da aka yi masa.