An kama ‘yan fashi 13 da kwato motoci 4 a Zamfara

Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tayi nasarar kame ‘yan fashi da makami 13 tare da kwato motoci 4 da suka sace da tarin makaman da suke amfani da su wajen aikata miyagun aiyuka a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Usman Nagode, ya shaidawa manema labarai cewa an samu bindiga kirar pistol da harsashenta a hannun ‘yan fashin an kuma gano motoci guda 4 da suka sata tare da tarin baburan acaba.

Ya ce, an gano kayayyakin ne a gidajen ‘yan fashin a binciken da rundunar ke ci gaba da yi a kan su, inda aka gano wasu daga cikin motocin a garin Suleja na jihar Neja da kuma mota kirar Hilox da ‘yan fashin suka sace a gidan Daraktan Ma’aikatar Samar da Guraben Ayyuka na jihar Zamfara wacce suka kai kasar Nijar suka sayar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya