✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ‘yan fashi bayan sun shiga banki a Abuja

Wasu ‘yan fashi da makami sun shiga bankin First Bank da ke Mpape a Abuja, sai dai kafin su kammala abin da ya kai su…

Wasu ‘yan fashi da makami sun shiga bankin First Bank da ke Mpape a Abuja, sai dai kafin su kammala abin da ya kai su sai ‘yan sanda da sojoji suka yi musu kofar rago yau da safe.

Rahotan na bayyana cewa ‘yan fashin suna cikin bankin sun kasa fitowa, inda har aka harbi daya daga cikinsu a yayin da yake kokarin guduwa sannan sun kuma kama mutum hudu da ake zargi, ‘yan sanda da sojoji sun zagaye yankin wajen da bankin yake a yayin da ‘yan fashin ke cikin bankin.