✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kame ‘yan IPOB 33 akan zargin kisan jami’in dan sanda

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra su 33 bayan sun kai wa jami’anta hari…

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra su 33 bayan sun kai wa jami’anta hari tare da kashe Sufeta daya.

Kakakin Hukumar ‘yan sanda na jihar Anambra DCP Jimoh Moshood ne ya sanar da hakan kuma ya ce, kuma ya ce an kame wadanda ake zargin ne a Anambra.

Za a dai gurfanar da wadanda ake zargin a kotu don tuhumarsu akan zargin kisan jami’in dan sandan.