✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kame ‘Yan Kungiyar asiri 16 a Benuwe

Rundunar ‘Yan sandan jihar Benuwe ta kama wasu mutum 16 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, wanda suka haddasa mutuwar jama’a da dama a…

Rundunar ‘Yan sandan jihar Benuwe ta kama wasu mutum 16 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, wanda suka haddasa mutuwar jama’a da dama a cikin wata daya daga yankuna daban daban na jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ya ce an kama wadanda ake zargin ta hanyar samun bayanan sirri da jami’an suka samu kuma ake zaton su ne suka haddasa kisan gillar jama’a da dama a cikin wata daya tare da asarar dukiyoyi masu yawa a jihar.

DSP Catherine, ya bayyanawa manema labarai a Hedkwatar Rundunar ‘yan sandan da ke Makurdi babban birnin jihar cewa, an kama mutum 12  daga cikin su a tashar mota suna hanyar su ta zuwa kauyen Adaka daidai hanyar garin Naka don binne wani dan uwansu da wasu ‘yan kungiyar asirin suka kashe.

Yayin da sauran 4 aka kama masu a maboyarsu, an kama su da bindiga kirar pistol.