✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Ali Nuhu digirin girmamawa na Dokta a Togo

Jami’ar ISM Adonai American Unibersity da ke birnin Kwatano a Jamhuriyyar  Benin ta karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu da digiririn digirgir na girmamawa…

Jami’ar ISM Adonai American Unibersity da ke birnin Kwatano a Jamhuriyyar  Benin ta karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu da digiririn digirgir na girmamawa wato Dokta.

An karrama jarumin ne a yayin taron lacca da bikin yaye dalibai da ba da kyaututtuka na shekarar 2017/2018 da Jami’ar ISM Adonai ta shirya a dakin taro na Palaise De Congress da ke birnin Lome a kasar Togo a ranar Lahadin da ta gabata.

A lokacin da yake jawabi a wurin taron, Magatakardar Jami’ar, Dokta Adamu Muhammad ya ce jami’ar ta ba Ali Nuhu digirin Dokta ne kan sana’o’i da taimakon matasa sakamakon jajircewarsa wajen tallafa wa daruruwan matasa a tsawon shekara 20 da suka gabata don su tsaya da kafafunsu.

Ya ce, “Wannan gudunmawa da ka bayar ba boyayyiya ba ce a duniya, kuma hakan ya sa Majalisar Gudanawar Jami’armu ta ga dacewar ta karrama ka da digirin Dokta.”

Dokta Muhammad ya kara da cewa jami’arsu ta gamsu da yadda Ali Nuhu yake taimakon matasa da aikin yi da kuma yin fina-finan da suke farkar da matasa wajen neman aikin yi.

A lokacin da yake jawabin godiya, Ali Nuhu ya nuna farin cikinsa kan yadda jami’ar ta gano irin gudunmawar da yake ba matasa wajen ganin sun tsaya da kafafunsu.

Ya ce, “Abin alfahari ne gare ni kan wannan shaidar ta Dokta da aka ba ni. Ina mika godiyata ga Majalisar Jami’ar ISM Adonai American Unibersity, Ina kuma gode wa masoyana wadanda suke yi mini fatan alheri.”

A cikin ’yan fim din da suka yi wa Ali Nuhu rakiya akwai Abubakar S. Mohammed da Umar Gombe da Is’hak Ahmad da Rashidoo da sauransu.