Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An karrama masu tallafa wa al’umma a yankin Toro

Sashin Kiwon Lafiya na Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ya karrama wadansu fitattun mutane kan kokarin da suke yi wajen tallafa wa harkokin kiwon lafiya a yankin.

Mutanen da aka karramar sun hada da Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Danlami Garba Abubakar da Alhaji Saleh Sani  da Alhaji Sunusi Khalifah da Alhaji Yusuf Adamu Kegga da ma’aikatan asibitin kauyen Nahuta da kuma  Ardon Falama, Yusuf Ubandoma.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Sashin Kiwon Kafiya na Karamar Hukumar, Alhaji Ahmed Ibrahim Umar ya bayyana cewa ganin yadda wadannan mutane suke bayar da tallafi kan kiwon lafiya a yankin ya sanya sashin ya zakulo su kuma ya karrama su, ya nuna musu godiya kuma da karfafa musu gwiwa.

Ya ce kamar Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Danlami Garba Abubakar, an karrama shi ne kan yadda yake bai wa harkokin kiwon lafiya muhimmanci, a karamar hukumar.

ADVERTISEMENT

Ya ce tun da Shugaban ya fara shugabancin karamar hukumar, karo na uku ke nan yana bai wa harkokin kiwon lafiya muhimmanci. Ya ce ya gina asibitoci da gidajen malaman asibitoci tare da gyara asibitoci da dama a karamar hukumar.

Kuma ya ce an karrama Alhaji Sale Sani da Alhaji Sunusi Khalifa ne kan kokarin da suka yi wajen tallafa wa asibitin garin Rishi. “Wadannan mutane sun saya wa wannan asibiti katifu da gyara motar daukar marasa lafiya da gina bayan gida a asibitin da daukar ma’aikata suna biyan su albashi a asibitin,” inji shi.

Haka kuma ya ce an karrama ma’aikatan asibitin kauyen Nahutan Taba ne saboda kokarin da suka yi wajen tara Naira dubu 432 da inganta ayyukan asibitin.

“Ardon Falama Yusuf Ubandoma, an karrama shi ne kan kokarin da yake yi wajen ganin mutanen kasarsa sun karbi rigakafi,” inji shi.  A yayin da aka karrama Alhaji Yusuf Adamu Kegga kan kokarin da yake yi wajen aikin kiwon lafiya, a matsayinsa na ma’aikacin kiwon lafiya na karamar hukumar.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar su yi koyi da wadannan mutane wajen tallafa wa harkokin kiwon lafiya a karamar hukumar ta Toro.