✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe barayi 3 tare da babbakasu a motarsu a Abuja

Wasu mutum 3 da a ke zargin masu yin fashi a cikin mota ne da a ka fi sani da suna “Wan cans” sun gamu…

Wasu mutum 3 da a ke zargin masu yin fashi a cikin mota ne da a ka fi sani da suna “Wan cans” sun gamu da ajalinsu a Abuja, inda a ka kashesu tare babbakasu a cikin motar da su ka dauko wata mata a ciki.

Lamarin ya faru ne a yau Litinin da misalin karfe 8 na safe a karkashin wata Gadar mahadar-hanya da ta nufi Garin Dutsen-Alhaji, a kan babban titin Kubwa Abuja.

Wasu da su ka zanta da wakilinmu a wajen sun bayyana cewa, matar ta yi ta ihun neman taimako bayan barayin sun yi yunkurin hankadota daga cikin motar a daidai lokacin da su ka iso karkashin gadar, wadda keda yanayin kewa.

Wani da ya shaidi lamarin ya ce, ’yan acaba da ke aiki ta wajen sun nufi kan motar tare da tareta bayan shawo kwana daga hanyar samar, lamarin da ya tilastawa barayin fita daga cikin motar sannan su ka yi yunkurin tserewa.

“Nan take gungun jama’a su ka auka masu kuma bayan an jikkatasu sai aka turasu ta jikin motar wadda ke ci da wuta, in ji shi.

Haka nan kuma an kona wata mota ta biyu da ake zargin wanda ke tukata na tare da barayin, a daidai mahadar phase 3 na Garin Kubwa da titin ta bi.

Wasu matasa ke kokarin kawar da motar barayin daga inda a ka konasu tare da motarsu