✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sarki a fadarsa a Taraba

’Yan bindiga sun kashe Sarkin Sansani da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, , Alhaji Abdulmudallib Kankada.

’Yan bindiga sun kashe Sarkin Sansani da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Abdulmudallib Kankada.

Maharan sun shiga fadar Sarkin mai daraja ta uku ne da misalin karfe 9 na daren Alhamis, inda suka yi masa ruwan harsashi, suka kashe shi nan take.

Wani mazaunin garin na Sansani mai suna Musa, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa a cikin dakin Sarkin ’yan bindigan suka kashe shi.

A cewarsa, a  kan babura suka shiga garin, amma suka boye buburan nesa da fadar sarkin suka shiga ba tare da kowa ya sani ba.

Ya ce daya daga cikin matan sarkin ce ta shiga dakin ta tarar da an kashe mijin nata yana kwance cikin jini, shi ne ta sanar wa sauran matan daga nan kuma labarin ya bazu cikin gari.

Musa ya ce bayan Sallar Juma’a za a yi jana’izar sarkin a fadarsa.

An taba sace sarkin shekarun biyu da suka wuce kuma sai da aka biya kudi aka sako shi.

Sarkin Sansani shi ne a bakwai a jerin sarakunan gargajiya da ’yan bindiga suka halala a ’yan shekarun nan a Jihar Taraba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, David lloyanomon, da wakilin Aminiya ya kira shi kan wannan lamarin, ya ce ya tuntubi kakakin rundunar, SP Usman Abdullahi, wanda shi kuma ya ce bashi da lafiya ba zai yi magana ba.