✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Mataimakin shugaban Abaji bayan biyan kudin fansa

‘Yan bindiga da suka yi garkuwa da Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Rizoma, sun kashe shi bayan karban kudin…

‘Yan bindiga da suka yi garkuwa da Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Rizoma, sun kashe shi bayan karban kudin fansa da suka bukata na Naira miliyan 3.

Wani dan uwan Rizoma ne ya tabbatar wa majiyar mu ta wayar tarho rasuwar Mataimakin Shugaban Abaji.

Rahotan ya kara da cewa, masu garkuwa sun kashe Rizoma ta hanyar dukansa lokacin da yake yunkurin tsere wa daga dajin da aka tsare shi ranar daren Talata da ta gaba ta.

Masu garkuwan sun kama Mataimakin shugaban Karamar hukumar da direbansa Hussaini Peter da dansa Mohammed Yakubu har zuwa ranar Litinin yayin da aka biya kudin fansa ranar Alhamis.

Rahotan ta kara da cewa, masu garkuwan sun yi barazanar kashe direba Husaini  da dan Mohammed Rizom idan suka sanar da rasuwar Mataimakin shugaban Karamar hukumar Abaji.