✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matashi kan budurwa a Kano

Al’ummar Unguwar Sheka a Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano sun wayi gari da alhinin mutuwar wani dan unguwar, Sagir Muhammad wanda aka zargi matashi…

Al’ummar Unguwar Sheka a Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano sun wayi gari da alhinin mutuwar wani dan unguwar, Sagir Muhammad wanda aka zargi matashi Abdullahi Muhammad da kashewa.

Ana zargin Abdullahi ya kashe Sagir Muhammad dan kimanin shekara 22 ta hanyar dukan sa, saboda samun sabani da suka yi a kan wata budurwa.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa rigima ce ta auku a tsakanin matasan biyu a kan wata budurwa da ke unguwar.

Majiyar ta ce bayan da lamarin ya faru an garzaya da marigayin wata karamar cibiyar lafiya da ke unguwar ta Sheka inda kuma a nan ne rai ya yi halinsa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kai.