Search
Subscribe
An kashe mutum 8 da yin garkuwa da Hakimi da wasu 6 a Neja

An kashe mutum 8 da yin garkuwa da Hakimi da wasu 6 a Neja

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari jiya Talata da safiyar yau Laraba a unguwanni biyu da ke cikin Karamar Hukumar Rafi da ke jihar Neja. Inda suka kashe mutum takwas lokaci daya sannan suka yi garkuwa da Hakimin Madaka, Alhaji Zakari Yau tare da matarsa, da Mai Unguwan Kukoki tare da wasu mutum hudu. Kamar yadda mazauna uguwannin suka sanar.

“‘Yan bindigar sun yi awon gaba da Sakataren gundumar da wani soja mai ritaya.” Kamar yadda majiyarmu ta samu rahoton.

Matar Hakimin da aka sace tana shayar da jariri kuma suka yi awon gaba da ita da jaririn.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin