✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sojoji 2, an kona gida 150 a Filato

Mahara sun  kashe sojoji 2 da suke aiki da Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa a Jihar Filato (OPSH) a daren Lahadin da ta gabata, a kauyen…

Mahara sun  kashe sojoji 2 da suke aiki da Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa a Jihar Filato (OPSH) a daren Lahadin da ta gabata, a kauyen Gindin Akwati da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato.

Sakamakon wannan al’amari ana zargin sojoji da suke aiki a rundunar da kone gidajen Fulani 150, a ranar Talatar da ta gabata.

Da yake zantawa da wakilinmu kan lamarin Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Karamar Hukumar Barikin Ladi Alhaji Shu’aibu Bayaro, ya yi zargin cewa sojojin da suke aiki a rundunar a cikin motoci 4 kirar Hilud da babura 11 sun isa kauyukan Dogon Yelwa da Hayi da Marabar Gindin Akwati da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi suka kone gidajen Fulani.

“Wannan abu ya ba mu mamaki ganin cewa Kwamandan Rundunar OPSH na Gundumar, Manjo Gado ya kira shugabannin al’ummar wannan yanki kan sojojin da aka kashe, inda aka yi zama da su, kuma suka bayar da tabbacin za a binciko wadanda suka aikata wannan al’amari. Ya bukaci mu ba shi hadin kai wajen ganin an gano wadanda suka aikata wannan mugun aiki, kuma mun amince za mu ba su hadin kai amma abin mamaki sai muka wayi gari da wannan abu,” inji shi.

A lokacin da aka tuntubi Kakakin Rundunar OPSH, Manjo Ibrahim Shitu ya ce zuwa lokacin bai samu wannan labari ba. Amma wata majiya ta rundunar a kauyen Gindin Akwatin ta tabbatar da cewa an harbe jami’anta biyu a yankin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel ya tabbatar da labarin harin da aka kai wa soja a yankin,  amma ya ce bai samu rahoton kone gidajen Fulanin ba.