✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wanda ya shirya yin garkuwa da shugaban UBEC

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce, jami’an su sun kashe wanda ya shirya yin garkuwa da shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (UBEC) Dakta Mohammed…

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce, jami’an su sun kashe wanda ya shirya yin garkuwa da shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta kasa (UBEC) Dakta Mohammed Mahmood Abubakar da ‘yarsa Yasmin.

An yi garkuwa da shugaban UBEC a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar 29 ga watan Afrilu 2019.

Kakakin hukumar  ‘yan sanda  DCP Frank Mba, ne  ya sanar da hakan, kuma ya ce sun jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar kama wasu da suka shahara a fannin yin garkuwa da mutane da suka hada da: Sumaila Sule da Alias Shaho, wadanda suke zaune a kauyen Rijana da ke karamar hukumar  Kachiya jihar Kaduna.