✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kubutar da mai hidimar kasar da aka yi garkuwa da ita a Legas

Jami’an Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas a karkashin jagorancin Kwamishinanta, Hakeem Odunmosu, sun yi nasarar kubutar da wata mai yi wa kasa hidima (NYSC) daga…

Jami’an Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas a karkashin jagorancin Kwamishinanta, Hakeem Odunmosu, sun yi nasarar kubutar da wata mai yi wa kasa hidima (NYSC) daga hannun masu garkuwa da ita a tsaunin daji da ke kewaye da ruwa a shiyyar Epe a Jihar Legas.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, jamai’an rundunar sun yi ba-ta- kashi da masu garkuwa da mutanen a wani tsauni mai sarkakiya inda suka ceto mai hidimar kasar mai suna Onyiwara Chinwe Faith. Ya ce tana yi wa kasa hidima ce a gonar ABC da ke yankin Ilamija Nila, kana masu garkuwar sun kama ta ce a ranar Juma’ar makon jiya inda suka nemi Manajan Gonar ya biya kudin fansa Naira miliyan daya daga bisani su rage zuwa Naira dubu 400.

“Jami’anmu sun yi nasarar ceto ta, ba tare da an biya kudin fansa ba, bayan musayar wutar da suka yi da masu garkuwar inda suka yi nasarar kama mutum daya, wanda shi ne jagoransu mai suna Moses Ofeye da ke zaune a Jihar Ondo, amma dan asalin Ijaw daga Neja-Delta,” inji shi.

Ya ce, an garzaya da ita asibiti inda aka binciki lafiyarta lura da zullumi da tafiya a kasa da masu garkuwar suka sanya ta, inda daga bisani rundunar ta mika ta ga Hukumar NYSC wacce za ta mika ta ga iyayenta.