✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kusa binne amarya da ranta

Al’ummar Unguwar Galma da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, sun cika da mamaki tare da alhini kan labarin rasuwar wata amarya, mai suna Jamila…

Al’ummar Unguwar Galma da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, sun cika da mamaki tare da alhini kan labarin rasuwar wata amarya, mai suna Jamila Abubakar; wadda makwanni biyu ke nan da daura aurenta amma daga baya  aka samu ta farfado bayan an kammala dukkan shirye-shiryen yi mata jana’iza, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, angon amaryar, Malam Muhammad Sani Kaura Mai Hoto ya bayyana cewa shi dai ya tashi da amaryar tasa a ranar Juma’ar da ta gabata da safe lafiya, babu abin da yake damunta.

Ya ce da misalin karfe 8 zuwa 9 na safe, sai ya ce mata zai tafi Jos daurin auren wasu abokansa, amma zai dawo da yamma ko da safe. Suka yi sallama ya shiga cikin garin Saminaka domin ya gabatar da wani uziri, kafin ya tafi.

Ya ce sai kawai aka kira shi a waya aka ce masa matarsa ta rasu, a ina za a yi jana’iza? Sai ya ce ta rasu bayan ya bar ta a gida lafiya? Ya ce sai aka ce masa cikinta ne yake ciwo, har ya kai ga rasuwarta.

Muhammad Sani ya bayyana cewa, “ina zuwa gida sai na tarar da mutane maza da mata sun cika gidan babu masaka tsinke.”

Ya ce bayan da ya shiga dakin da aka kwantar da ita, ya je ya daga ta, ya duba, sai ya ga ta nuna dukkan alamu na mai mutuwa, babu numfashi ga baki daya kuma an lullube ta.

Ya ce lokacin da wannan abu ya faru, har an kira wani likita yazo ya sanya mata ruwa, sai aka cire aka ce ta riga ta mutu. Ya ce wannan abu ya faru ne tun wajen misalin karfe 12; 30 na rana har zuwa karfe 4:52 na yamma ba ta farfado ba.

“An riga an sallama cewa ta mutu, an aika wa ’yan uwa a garuruwa daban-daban, ana ta zuwa domin a yi mata jana’iza. An tura a je a haka ramin kabari. Wani ikon Allah ana cikin wannan hali, sai wani ya shigo ya ce ta fara numfashi kadan-kadan, a saurara. Ba a fi minti 15 da saurarawar ba, kawai sai aka ga ta bude idonta. Da ta ga mutane sai ta ce lafiya?”

Ya ce a gaskiya ya yi matukar farin ciki da farfadowar Amaryar tasa, domin lokacin da ya zo ya same ta  kwance, har ya cire rai amma da aka ce ta farfado sai murna da farin ciki suka lullube shi. Ya ce tun daga lokacin da ta farfado har ya zuwa wannan lokaci, komai

lafiya tana cin abincinta kuma tana cikin walwala.

Da take zantawa da wakilinmu, amarya Jamila Abubakar ta bayyana cewa a ranar juma’ar da ta gabata da safe, da misalin karfe 10, ciwon ciki da zazzabi ya kama ta. Ta ce tun daga wannan lokaci ba ta san abin da ya faru ba, sai kawai ta tashi ta ga mutane sun yi cincirindo a kanta.

Ta ce bayan da ta farfado, abin ya ba ta mamaki kwarai da gaske, domin sai tana jin kamar ba ita ba ce. “A gaskiya tun da na farfado, ban sake jin wata damuwa a jikina ba. Amma har yanzu mutane suna zuwa gaisuwa, kan cewa na mutu,” inji ta.

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, wani abokin agon, Abubakar Atiku Dayyabu ya bayyana cewa suna tafiya a cikin gari, sai suka hadu da wata yarinya, sai ta ce masu Allah Ya yi wa amarya Jamila rasuwa. “Daga nan muka karaso gidan muka yi alwala muna jiran a fito da ita, domin mu yi mata Sallah. An ajiye ruwa a baho za a yi mata wanka, mun zauna muna jira sai aka ce ta farfado har ta fara magana.”

Dokta Mannir Sani ya bayyana cewa a tsarin likitanci irin na zamani, akwai abubuwan da ake dubawa kafin a tabbatar da cewa mutum ya mutu. Ya ce haka kawai don ka taba mutum ka ga ba ya motsi, ba za ka ce ya mutu ba, sai ka duba wadannan wurare ka tabbatar, kafin ka ce mutum ya mutu.

“Akwai wasu bangarori na jikin dan Adam da ake dubawa kafin a tabbatar da cewa mutum ya mutu. Na farko shi ne numfashi, ma’ana kirjinsa yana bugawa ko ba ya bugawa? Abu na gaba shi ne a duba zuciyarsa, shin tana harba jini? Abu na gaba shi ne, a duba kwakwalwar mutumin, ta hanyar bude idon mutumin a gani, domin akwai abubuwan da za gani a kwayar idon da za su tabbatar cewa kwakwalwar mutumin ba ta aiki. Idan aka sami wadannan abubuwa ba su aiki, shi ne zai tabbatar cewa mutum ya mutu,” inji likitan.

Ya ce a bayani da aka yi kan wannan mata, ta yi dogon suma ne, ba mutuwa ba, domin ’yan uwanta ba su yi wannan bincike sun tabbatar ba.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi babban Limamin Masallacin Juma’a na Kamfa da ke garin Saminaka, Malam Muhammad Aminu Muhammad kan wannan al’amari, cewa ya yi Allah ne ya nuna ayarsa kan wannan

al’amari. Ya ce Allah Ya nuna cewa tun dama rayukan al’umma  suna hanunSa ne, yana iya rike rayuwar mutum na wani tsawon lokaci, shi bai mutu ba kuma ba ya cikin rayuwa, wadda za a iya yin magana da shi, ko ya iya sarrafa wani abu.

“A Musulunci, irin wannan doguwar suma tana faruwa, sai dai kawai ya kamata mutane su dauki darasi. Idan har aka ga numfashin mutum ya dauke babu alamar rayuwa tattare da shi, kafin a yanke hukuncin cewa ya rasu, a yi kokarin ganin kwararrun likitoci, domin su tabbatar da rasuwarsa. Idan ana yin haka, za a samu saukin irin wannan matsala,”