✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Barista Nasiru Dembo a matsayin Gado da Masun Lere

Mai martaba Sarkin Lere da ke Jihar Kaduna Birgediya Janar Garba Abubakar Muhammad Mai ritaya ya nada Barista Nasiru Bello Dembo a matsayin Gado da…

Mai martaba Sarkin Lere da ke Jihar Kaduna Birgediya Janar Garba Abubakar Muhammad Mai ritaya ya nada Barista Nasiru Bello Dembo a matsayin Gado da Masun Masarautar Lere, a fadarsa da ke garin Lere a ranar asabar din da ta gabata. 

Har’iya yau a wannan ranar, Mai martaba Sarkin na Lere ya nada Alhaji Umaru Musa a matsayin Sarkin fadar Lere da Alhaji kasimu a matsayin Makama Babba da Aliyu Ibrahim Pate a matsayin Sarkin Dawaki mai tuta da kuma Injiniya Halliru Abubakar a matsayin Tafarkin Lere. 

Da yake jawabi mai martaba Sarkin Lere Birgediya Janar Garba Abubakar mai ritaya ya bayyana cewa an nada wadannan mutane ne saboda ganin cancantarsu da kuma halayen iyayensu. 

Ya ce iyayensu sun yi kokari sun bayar da gudunmawa a wannan masarauta, ta yadda muka kai inda muke a yau. Don haka muna fatar zaku yi koyi da halayen iyayenku a wannan masarauta. 

Ya ce “muna fatar za ku ci gaba da bayar da gudunmawarku wajen cigaban wannan masarauta.” 

Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala nadin sabon Gado da Masun Lere Barista Nasiru Bello Dembo ya bayyana farin cikinsa kan wannan nadi da aka yi masa. 

Ya ce “wannan wata rana ce ta farin ciki a gareni, wadda ba zan taba mantawa da ita ba. Sabo a wannan rana ce an aka min wannan nadina Gado da Masun Lere.  

Sannan ya bada tabbacin cewa zai ci gaba da tallafawa ‘ya’yan wannan masarauta  kamar yadda ya saba, don ganin an sami ci gaba mai dorewa a wannan masarauta, “Zan yi amfani da wannan sarauta domin ci gaba da bayar da gudunmuwa kamar yadda na saba wajen ciyar da masarautar Lere da jama’ar masarautar gaba,” in ji shi.

Shi dai Barrista Nasir Bello Dembo kwararran lauya ne da ke aiki da Hukumar Yi wa Kamfanoni Rigista ta kasa (CAC). Ya yi makarnatar Firamare da Sakandare a makarantar Kaduna Capital. Ya samu digirinsa na farko a fannin karatun lauya a shekarar 2005 a jami’ar Bayero da ke Kano, sannan ya yi digiri na biyu a fannin karatun lauya a shekarar 2011. Hakanan kuma Barista Nasir ya kara samun wani digirin na biyu a shekarar 2017. Sannan kuma memba ne a kungiyoyi da dama da suka hada da memba na kwamitin amintattu na kungiyar ENDS, tsarin tallafawa matasa na link da dai sauransu.