✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Dokta Shamsudden Aliyu Garkuwan Makarantar Zazzau

A makon da ya gabata ne Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya nada Dokta Shamsuddeen Aliyu a matsayin Garkuwan Makarantar Zazzau a fadarsa da ke…

A makon da ya gabata ne Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya nada Dokta Shamsuddeen Aliyu a matsayin Garkuwan Makarantar Zazzau a fadarsa da ke birnin Zazzau.

An nada Dokta Shamsuddeen bisa la’akari da yadda yake bayar da gudunmuwa wajen cigaban ilimi a lardin Zazzau da ma kasa baki daya.

Da yake zantawa da wakilin Aminiya, Dokta Shamsudden ya ce “Saboda son tallafa wa ilimi da masu ilimi shi ya sa na kafa makaratu guda 471. Dukan makarantun sun fara ne daga matakin Naziri zuwa Difloma, kuma ana rubuta jarabawar kammala Sakandare na WAEC da NECO, sannan kuma yawancinsu na kwana ne,” in ji shi.

Shi dai Dokta Shamsuddeen Aliyu yana da digiri har tara a fannoni daban-daban da suka hada da fannin Koyar da ilimin kimiyya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Industrial Chemistry a Jami’ar Bayero da ke Kano, da wadansu da ya yi a nan kasa Najeriya da kuma kasashen waje kamar su Sudan, Misra da Dubai. sannan kuma yana da digirin digirgir a fannin kimiyyar hada magunguna wato Pharmacy.

“Na yi digiri guda tara a fannonin ilimi daban-daban. Yadda nake yi shi ne, nakan duba bangaren da ya fi wahala, inda dalibai suke shan wahala wajen koya, sai in je in karanto fannin domin in koyar da dalibai cikin sauki.”

Da ya koma kan dalilin da ya sa masarautar Zazzau ta nada shi Garkuwan Makaranta kuwa, Dokta Shamsudden cewa ya yi, “Kafa makarantu da taimakon dalibai masu son karatu musamman marayu, da kokarin tabbatar da zaman lafiya shi ne dalilin da ya sa masarautar Zazzau ta ga na dace ta nada ni wannan sarauta ta Garkuwan Makaranta.”