✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sabon Sarkin Yarbawan Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke Jihar Kaduna,  Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada  Abdullatif Abdulsalam Muhammad Bello a matsayin sabon sarkin Yarabawan  Saminaka. Ya…

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke Jihar Kaduna,  Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada  Abdullatif Abdulsalam Muhammad Bello a matsayin sabon sarkin Yarabawan  Saminaka. Ya nada Sarkin Yarbawan ne a makon jiya a fadarsa da ke Saminaka.

Da yake jawabi lokacin nadin, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya ce nadin na  Sarkin Yarbawa, an dada jaddadawa ne. Domin marigayi tsohon Sarki ne ya fara nada mahaifin sabon Sarkin na yanzu lokacin da yake raye. Ya ce ganin Allah Ya yi wa Sarkin Yarbawan  rasuwa, ya sa aka nada sabon Sarki. Kuma al’ummar Yarbawan masarauta ne suka bukaci a nada sabon Sarkin nasu.

Sarkin Saminka ya ce al’ummar Yarbawa mutane ne da suka dade a garin Saminaka. Kuma suna zaune da al’ummar garin lafiya, suna yin dukkan harkokin rayuwa tare da  su. Sai ya yi kira ga al’ummar Yarbawan da dukkan al’ummar masarautar su ci gaba da zama lafiya, domin a samu ci gaba a masarautar.

Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala nadin, sabon Sarkin Yarbawan Abdullatif ya mika godiyarsa ga Allah sannan da Mai martaba Sarkin Saminaka kan wannan nadi da aka yi masa.

Ya ce tun mahaifunsu yana raye ya yi da shi ya karbi wannan sarauta, amma ya ki  har zuwa lokacin da ya rasu. Ya ce bayan rasuwar mahaifin nasu ne, ya ga alamar wadansu sun nuna suna son wannan sarauta, shi ne ya nuna shi ma yana so, kuma Mai martaba Sarkin Saminaka ya amince aka nada shi.

Ya ce zai ci gaba da dorawa daga inda mahaifinsa ya tsaya, wajne hada kan dukkan al’ummar Yarbawa tare da sauran al’ummar masarautar.

Ya yi kira ga dukkan al’ummar Masarautar Saminaka kan su ci gaba da zaman lafiya da hadin kai domin samun nasara a masarautar.