Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An nada ’yar Najeriya a matsayin Minista a Birtaniya

Olukemi Badenoch

An nada ’yar Najeriya a matsayin Minista a Birtaniya

Sabon Firayi Ministan Birtaniya, Mista Boris Johnson, ya nada wata ’yar Najeriya mai suna Olukemi Badenoch da aka haifa a Birtaniya, a matsayin Karamar Ministar Yara da Iyali.

Nadin nata wani yunkuri ne da sabon Firayi Ministan ke yi don yi wa gwamnatinsa garambawul.

Misis Badenoch dai ta kasance ’yar Jam’iyyar Conserbatibes ce mai ra’ayin rikau, daga mazabar Saffron Walden a Birtaniya.

’Yar siyasar mai shekara 39, an haife ta ce a yankin Wimbledon a birnin Landan kuma iyayenta ’yan Najeriya ne. Kuma ta taso ne a birnin Legas da Amurka, amma ta koma Birtaniya yayin da take da shekara 16.

Wani lokaci a baya, ta taba yin tsokaci a gaban Majalisar Dokokin Birtaniya game da yadda ta yi fama da kuncin rayuwa da kuma yadda ta yi ta amfani a-ci-balbal wajen samun haske yayin da aka ba ta aikin gida a makaranta.

Ita dai Injiniyar Manhajar Kwamfuta ce da Fasahar Sadarwar Zamani, ta kuma yi karatu ne a Jami’ar Sussed a Ingila kuma tana da digiri a fannin shari’a. Ta yi aikin banki a yankin Coutts da RBS; sa’annan tana da ’ya’ya biyu.

Ta yi shelar nadin nata ne, ta shafinta na Tiwita a ranar Talata, inda ta rubuta cewa:

“Cikin kankan da kai, ina farin cikin sanar da nada ni a mukamin Minista a Ma’aikatar Yara da Iyali. Wannan babbar dama ce gare ni; da in yi wa jama’a aiki, tare da kawo sauye-sauyen da suka kamata a kan abubuwan da suka yi mini tsaye a rai.”

“Ina sa ran aiki tare da sauran ’yan Majalisar Zartarwa da kowa da kowa a Ma’aikatar Ilimin Birtaniya. Ina kuma godiya da irin sakonnin fatan alheri da taya murna da nake ta samu daga abokan arziki. Zan kuma yi aiki, ba kawai tare da ’yan jam’iyarmu ta Conserbatibes ba; har ma da sauran jam’iyyu,” inji ta.

An taba zabenta a matsayin ’yar majalisa a karon farko daga mazabar Walden Saffron, a ranar 8 ga Yunin 2017; kuma mace ta farko da ta taba wakiltar mazabar, a Majalisar Dokokin Birtaniya.

Ga wasu muhimman ababuwa da ba a sani ba game da rayuwarta:

  1. Ta fadi zaben Majalisar Birnin Landan; sai dai daga baya an ba ta kujerar bayan da wadansu mambobin majalisar biyu suka sauka daga kujerun a shekarar 2012.
  2. Ta yi ayyuka da daman gaske. Ta taba yin aiki a matsayin kwararriya da kuma jami’ar tuntuba a wasu kafofin kudade tare da yin aiki a matsayin Mataimakiyar Darakta a wani banki mai zaman kansa da kuma Manajar Kudi a Coutts; kafin ta zama Darakta a Mujallar Masu Ra’ayin Rikau ta The Spectator.
  3. Tana ’yar shekara 25 ta shiga Jam’iyar Conserbatibes, ta ’yan mazan jiya, tare da yin takara da ’yan jam’iyyun Labour da Liberal Democrat, ta masu sassaucin ra’ayi.
  4. An taba saka sunanta a lamba ta 96, a jerin ’ya’yan Jam’iyyar Conserbatibes 100 masu karfin fada-a-ji a shekarar 2017.
  5. Ta taba amincewa da yin kutse a shafin Intanet na wani dan majalisar Jam’iyyar Labour, a shekarar 2008; kuma an kai rahotonta ga Hukumar Action Fraud, mai kula da korafe-korafen shafukan Intanet.