✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli ya karbi sandar mulki

Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya karbi ratsuwar aiki da kuma sandar mulki.

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya karbi ratsuwar kama aiki a matsayin sarkin na 19.

A safiyar Litinin 9 ga Nuwamba, 2020, Limamin Kona, Alhaji Muhammad Aliyu, ya ba shi rantsuwar kama aiki sannan Gwaman Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mika masa sandar mulki.

“Ina rokon masu rike da sarautu, hakimai, da sauran ‘yan Majalisar Masarautar Zazzau da daukacin jama’ar masarautar da su mara wa sabon sarkin baya”, inji El-Rufai.

Sarkin Musulumi Muhammad Sa’ad Abubakar III, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi na daga cikin manyan sarkunan da suka halarci taron.

Da yake mika masa sandar mulki, El-Rufai ya ce mulki na Allah ne, Shi ke ba wa wanda ya ga dama.

Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa inda ya gaji surukinsa, marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, daga gidan Katsinawa.

Alhaji Shehu Idris ya jagoranci masarautar na natson shekara 45 daga shekarar 1975, kafin rasuwarsa sakamakon rashin lafiya a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Sarki Shehu Idris ya rasu ne a ranar 20 ga watan Satumban 2020, kafin a ranar 7 ga watan Oktoba a sanar da nada Ahmad Bamalli a matsayin magajin kujerar.

Kafin zamansa Sarkin Zazzau na 19, Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau, rawanin da mahaifinsa marigayi Nuhu Bamalli ya daura yayin da kakansa, Dan Sidi, shi ne sarkin Zazzau na 13, wanda ya yi sarauta tsakanin 1903 da 1920.

Kafin nadinsa, shi ne Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Thialand da kuma Myannmar.

Ya kasance Kwamishina na Dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna a shekarar 2015.

Ya yi aikin Banki har ya kai mukamin Babban Darakta sannan daga baya ya zama mukaddashin Manajan-Darakta a Hukumar Buga Takardun Kudi ta Najeriya.

Tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Birane ta Abuja kafin ya zama shugaban masu kula da ma’aikata a MTel, sashen sadarwa na tsohon Kamfanin Sadarwa na Nijeriya (NITEL).

Bamalli wanda aka haifa a ranar 8 ga Yuni 1966, ya yi karatun Lauya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sannan ya yi digiri na biyu a kan alakar kasa da kasa da diflomasiyya da kuma difloma kan jagoranci a Jami’ar Oxford.