✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa dokar dandake masu yin lalata da kananan yara a Amurka

Jihar Alabama da ke Amurka ta gabatar da sabuwar doka ga wanda duk aka samu da laifin yin lalata da kananan yara za a yi…

Jihar Alabama da ke Amurka ta gabatar da sabuwar doka ga wanda duk aka samu da laifin yin lalata da kananan yara za a yi masa dandaka, ta hanyar ba shi magani ko allurar rage sha’awar yin jima’i.

A wannan dokar, duk wanda aka kama da laifin yin lalata da karamar yarinya kasa da shekara 13 sai an fara ba shi magungunan rage yawan sha’awa na wasu watanni kafin a sako shi daga inda yake tsare.

A yanzu haka kotu ce za ta tabbatar ko akwai bukatar wannan dokar nan gaba ko ba bu.

Akwai jihohi bakwai wadanda suka hada da: Louisiana da Florida a Amurka wadanda duk suke da irin wannan dokar ga duk wanda aka samu da laifin yin lalata da karamar yarinya sai an basu magungunan rage saha’awar yin jima’i.

A ranar Litinin da ta wuce ne Gwamnan Alabama Kay Ibey, ta rattabawa kudirin dokar hannu.

“Wannan wani mataki ne kare rayuwar yara mata a jihar Alabama,” in ji Gwamnar.

Duk mai laifin da aka kama sai ya biya kudin maganin da aka yi masa. Dan majalisar wakilai na Jam’iyyar Republican Stebe Hurst, ne ya gabatar da kudirin dokar.

Stebe ya ce ya dade yana jin korafin kungiyar kare hakkin yara ta yadda ake cin zarafin ’yan mata kanana.

Sai dai Daraktan Kungiyar ’Yancin farar hula ta ’American Cibil Liberties Union of Alabama‘, Randall Marshall, ya soki kudirin dokar a kafar sadarwa ta AL.com. A sukar kudirin da Daraktan Kungiyar ya yi na cewa, wannan matakin baida wani alfanu saboda ba a tantance irin maganin ba.

“Idan har jihar ta fara yi wa jama’ar jihar amfani da irin wannan dokar, hakan zai iya kawo matsala ga dokokin kasar.

Maganin da zai rage sha’awar an yi shi ne ta hanyar kwaya da kuma ruwan allura wanda zai taimaka wajen rage sha’awar masu yin lalata da kananan yaran.

A shekarar 2009, an yi wa adadin fursunoni wadanda aka kama da irin wannan laifin magungunan rage sha’awar.

An dai ta gwajin maganin ga masu laifukan fyade.

Wani kwararre a fannin nazarin masu aikata laifuka mai suna Don Grubin, ya bayyana cewa wadanda aka yi wa magungunan sun samu canji a rayuwar su.

A shekarar 2016 kasar Indonesiya ta mika kudirin doka ga hukumomin kasar don yi wa masu yin lalata ga kananan yara maganin rage sha’awar da take sa su aikata hakan. A wannan lokacin wani likita daga cikin Kungiyar Likitocin Indonesiya, mai suna Prijo Sidipratomo, ya bayyana wannan maganin a matsayin abu mai cutarwa da kuma dakile ’yancin dan adam.

Kasar Koriya ta Kudu, ta kaddamar da dokar amfani da maganin rage sha’awa a watan Yuli 2011.