✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako jami’an FRSC biyu da aka yi garkuwa da su a Osun

Hukumar ‘yan sandan jihar Osun a yau Laraba sun tabbatar sako jami’an Hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC biyu da ‘yan bindiga suka yi…

Hukumar ‘yan sandan jihar Osun a yau Laraba sun tabbatar sako jami’an Hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Lahadi.

Kakakin hukumar ‘yan sandan shiyya DSP. Folashade Odoro, ne ya tabbatar da hakan bayan sako jami’an FRSC a Osogbo babban birnin jihar,  sai dai rahoton bai bayyana yadda aka sako jami’an. Kamar yadda majiyar kamfanin Dillancin labarai na Najeriya NAN ta sanar.