✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su a Akwa Ibom

A kalla masu yi wa kasa hidima 18 da suke yi wa Hukumar INEC aikin zabe aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban na Jihar…

A kalla masu yi wa kasa hidima 18 da suke yi wa Hukumar INEC aikin zabe aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban na Jihar Akwa Ibom ranar Asabar lokacin zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa lokacin da suke bakin aiki. Kwamishinan Hukumar INEC a jihar, Mista Mike Igini ne ya sanar da haka ga manema labarai a Uyo.

Da farko masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, lokacin da suke aiki da Hukumar INEC a wurare daban-daban na kananan hukumomin Abak da Ikot Ekpene mazabar tsohon gwamnan jihar Sanata Godswill Akpabio, inda aka kama mutum 10.

Yayin da hudu kuma aka sace su a Karamar Hukumar Ikono, sai hudu a Karamar Hukumar Itu.

Ya ci gaba da cewa, jin haka ke da wuya ya sanar da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar halin da ake ciki nan take ya ba za jami’ansa suka shiga nema kafin a tashi zabe aka sako mutum 10 daga cikin 18 da aka kama.

Ragowar hudu kuma daga baya aka sako su, amma bai yi bayani dangane da kudin fansa ba ko sun  ba masu garkuwa da mutanen kafin su sako masu yi wa kasar hidima ba.

Wakilin mu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Odiko MacDon game da garkuwa da masu yi wa  kasar hidima sai ya ce “Labarin bai iso mana ba, na yi magana da daraktan hukumar masu yi wa kasa hidima a jihar ya ce, ba shi da masaniya a kan hakan.”