✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sare hannuwan dalibi a Sakkwato

Wasu matasa sun shiga gidan wani dalibi da ke karatu a jami`ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato,  mai suna Habibu Abubakar, inda suka guntule masa hannuwa biyu.…

Wasu matasa sun shiga gidan wani dalibi da ke karatu a jami`ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato,  mai suna Habibu Abubakar, inda suka guntule masa hannuwa biyu.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar da daddare a unguwar Nakasari da ke birnin Sakkwato. Wadanda suka guntule hannuwan matashin sun shiga gidan ne dauke da makamai.

Habibu Abubakar ya ce, bayan sun sare min hannuwa sun tafi da bubur dina.

A yanzu haka, Habibu yana babban asibitin kashi da ke garin Wamako inda ake yi masa jinya.