✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare mahaifiyar da ta kashe jaririnta a Enugu

Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce, ta tsare wata mahaifiyar jariri mai suna Sandra Chisom Dimbo ‘yar shekara 21 wanda ake tuhumar ta da…

Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce, ta tsare wata mahaifiyar jariri mai suna Sandra Chisom Dimbo ‘yar shekara 21 wanda ake tuhumar ta da kashe jaririn da ta haifa lokaci kadan da haihuwarta.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Ebere Amaraizu ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya faru a a masaukin baki na Royal Lodgea unguwar Agbani a karamar hukumar Nkanu ta Yamma da ke jihar.

Amaraizu, ya ce, makwabtan matar sun ce sun ji kukan jaririn, amma ba su samu damar shiga dakin Sandra ba har sai da aka balle kofar sannan aka samu jaririn a mace.