✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa tsohon lauyan Donald Trump hukuncin daurin shekara 3

Wata babbar kotu a Manjattan, ta yanke wa tsohon lauyan Shugaban Amurka Donald Trump Michael Cohen hukuncin daurin shekara uku a gidan yari bayan ta…

Wata babbar kotu a Manjattan, ta yanke wa tsohon lauyan Shugaban Amurka Donald Trump Michael Cohen hukuncin daurin shekara uku a gidan yari bayan ta kama shi laifuffukan da suka hada da barnata kudade lokacin yakin neman zabe da tsallake haraji da kuma yi wa majalisa karya.

Da yake gabatar da hukuncin da ya yanke, alkalin kotun Mai shari’a William Pauley cewa ya yi, “An kama Cohen da laifuffukan da ba su kamata ba, wadanda ya kamata a matsayinsa na lauya a ce ya san su.”

Bayan a zaman gidan kaso da zai yi, Michael Cohen zai biya diyyar Dalar Amurka miliyan 1.39 da kuma Dala dubu 500 domin laifin barnata kudade a lokacin yakin neman zaben. Sannan zai biya wata diyyar ta Dala dubu 50 saboda karya da ya yi ga majalisar Amurka.

Shi dai Michael Cohen ya dade tare da Shugaban Amurka Donald Trump a matsayin na hannun damansa, inda ake ruwaito shi yana cewa, “Zan iya tare alburushin da aka harbo wa Trump.” Amma daga bisani da Cohen ya sha matsa daga wajen masu bincike, ya fitar da wasu muhimman bayanai da suka nuna abubuwan aibu game da yakin zaben Shugaba Trump da yanayin kasuwancinsa.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne lauyoyin gwamnatin Amurka suka fito fili suka bayyana cewa tsohon lauyan Shugaba Donald Trump, Michael Cohen ya cancanci a yanke masa hukuncin zaman gidan yari.

Lauyoyin sun aika wannan shawarar ce a cikin karar da suka gabatar wa kotu.