✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa ‘yan Faransa hukuncin kisa

Wata kotu a Iraki ta yanke wa wasu mutum uku ‘yan kasar Faransa hukuncin kisa, bayan samun su da laifin shiga kungiyar IS. Kamfanin dillancin…

Wata kotu a Iraki ta yanke wa wasu mutum uku ‘yan kasar Faransa hukuncin kisa, bayan samun su da laifin shiga kungiyar IS.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Kébin Gonot da Léonard Lopez da kuma Salim Machou.

An ba su damar daukaka kara cikin kwanaki 30.

Wadanda aka yanke wa hukuncin na daga cikin ‘yan kasar Faransa 12 da sojojin Amurka suka kama a kasar Syria.

A watan Fabrairu ne aka mayar da wadanda ake zargin zuwa Iraki, domin fara sauraren karar da aka shigar a kansu.

Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne ‘yan kasar Faransa na farko da ake zargi da shiga kungiyar IS da aka fara yanke wa hukuncin kisa.

Har yanzu dai Faransa ba ta ce komai ba dangane da hukuncin da kotun kasar Syriar ta yanke ba. Amma da aka matsa lamba kan lamarin a watan Fabrairu, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ki cewa komai dangane da lamarin sai dai ana ganin cewa lamari ne da kasar Iraki ke da iko a kai.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka soki wannan shari’ar, inda suka bayyana cewa kotun ta dogara ne da hujjojin da ta samu, bayan an tilasta wa wadanda ake zargin da su amsa laifinsu karfi da yaji.

Sai dai Lauyansu, Nabil Boudi ya yi watsi da wannan hukuncin da kotun ta yanke, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “wannan hukuncin an yi shi ne bisa irin tilasta wa wadanda ake zargin amsa laifinsu a gidajen yarin da ke Bagadaza a kasar ta Iraki’’