✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi bikin cika shekara 50 da zuwa duniyar wata a Amurka

Dubban Amurkawa sun yi bikin cika shekara 50 da nasarar kasar ta aikewa da mutanenta uku zuwa duniyar wata a ranar 16 ga watan Yulin…

Dubban Amurkawa sun yi bikin cika shekara 50 da nasarar kasar ta aikewa da mutanenta uku zuwa duniyar wata a ranar 16 ga watan Yulin 1969. Wavanda suka samu sukunin isa kan duniyar watan a harba su ne a cikin Kumbo Apollo 11, daga cibiyar hukumar NASA da ke birnin Florida.

A ranar Talata ce Buzz Aldrin mai shekara 89 da Micheal Collins mai shekara 88 suka sake havuwa a daidai wurin da suka tashi zuwa duniyar wata shekara 50 da suka gabata tare da kwamandansu Neil Armstrong da ya mutu a shekarar 2012, wanda shi ne na farko da ya soma taka duniyar wata.

Kumbon Apollo 11 ya shafe kwana huvu yana tafiya kafin ya isa kan duniyar wata a ranar 20 ga Yulin 1969.

Tun bayan kammala aikin mutanen uku da dawowarsu zuwa duniya a 1972, har yanzu babu kasar da ta sake samun nasarar aikewa da jami’anta zuwa duniyar wata.

A shekarun 1989 da kuma 2004 shugabannin Amurka George H.W Bush da vansa George W Bush suka yi alkawarin sake aikewa da tawagar bincike zuwa duniyar wata har ma da duniyar Mars, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, saboda rashin samun goyon bayan Majalisar Dokokin kasar a lokutan da suke mulki.

Za a shafe tsawon mako guda ana gudanar da bikin tunawa da ranar a Amurka.