✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da malamin jami’ar Ondo a jihar Edo

Masu yin garkuwa da mutane sun yi garkuwa da malamin jami’ar Kimiyya da fasaha ta jihar Ondo (OSUSTECH) Farfesa Gideon Okedayo da ke Okitipupa, a…

Masu yin garkuwa da mutane sun yi garkuwa da malamin jami’ar Kimiyya da fasaha ta jihar Ondo (OSUSTECH) Farfesa Gideon Okedayo da ke Okitipupa, a Ondo.

An yi  garkuwan da malamin ne a gabar hanyar Akoko daidai unguwar Igara zuwa Auchi a jihar Edo.

Kamafanin Dillancin Labarai NAN, ya bayyana cewa kimanin wata biyu kenan da samun rahoton garkuwa da mutane a jihar sai kuma kisan gillar da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne suka harbe Funke Olakunrin, mai shekara 58, wadda ‘ya ce ga shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Chif Reuben Fasoranti. A hanyar Ondo zuwa Ore da ke jihar Ondo a ranar 12 ga watan Yuli 2019.

Faruwar hakan yasa gwamnatin tarayya ta bada umarnin tsaurara tsaro a manyan hanyoyin jihar.