Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An yi garkuwa da masu ciki, likitoci da malamai a Ondo

Rahotanni daga Akure babban birnin jihar Ondo na cewa, an yi garkuwa da wasu likitoci masu ciki da wasu nas biyu da ke aiki a cibiyar lafiya ta tarayya a garin Owo da kuma wasu malaman kwalejin kimiyya biyu ta Rufus Giwa Polytechnic a hanyar Akure zuwa garin Owo jihar Ondo.

Daya daga cikin malaman da aka yi garkuwa da shi Taiwo Akinyemi ya ce, masu garkuwan sun bukaci kudin fansa Naira miliyan 100 kafin a sako shi. Kamar yadda majiyar Vanguard ta sanar.

ADVERTISEMENT