Da Dumi Dumi

An yi garkuwa da mutum 9 a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara ciki harda wani yaro mai shekara 12 a unguwar Pegi da ke Karamar hukumar Kuje cikin babban birnin tarayya Abuja.

An dai yi garkuwan da mutanen a daren jiya da misalin karfe 8:00, ‘yan bindigar sun shiga garin sanye da kayan soji.

Maharan sun harbi motoci biyu ciki akwai kananan motoci da suka hada da: kirar NISSAN Frontier da kirar Toyota Solara. Harsashi ya fasa tayoyin motocin.

Wani da ke cikin motar da aka harba na cikin mummunan hali. Ya kuma ce, akalla ‘yan bindigar sun kai mutum 20.

A safiyar yau Talata masu garkuwan sun bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 10 kafin a sako wadanda aka yi garkuwan da su.

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya