✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi gasar wasan damben gargajiya a kofar fadar Sarkin Zazzau

A ranan Asabar da ta gabata ce ’yan wasan damben gargajiya suka cika makil a kofar fadar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, domin taya…

A ranan Asabar da ta gabata ce ’yan wasan damben gargajiya suka cika makil a kofar fadar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, domin taya daya daga cikin ’ya’yan Sarkin, Dan Isa Zazzau Alhaji Umaru Shehu Idris murnar haihuwar ’ya mace. Fadar ta cika makil da ’yan kallo da bakin shahararrun ’yan damben gargajiya daga sassan kasar nan, wadanda suka hada ’yan wasa daga bangarorin daban-daban.

Akwai ’yan wasa bagaren Gura-mada da bagaren Arewa da bangaren Kudu. ’Yan wasan damben sun zo ne daga jihohin Legas Sakkwato da Zamfara da Kebbi  da Kano da Jigawa da kuma Birnin Tarayya, Abuja.

Mayan ’yan wasa ne suka fafata a wasanni daban-daban da aka yi, daga cikinsu akwai Kurumure na Dogon Auta wanda ya kara da Dan Yalo, sai Shagon Jamilu ya gwabza da Dan Libanda. Wasa na uku shi ne  wadda ya fi jan hankali tare da kayatarwa inda aka kece-raini a tsakanin Maitakwasara daga Gura-mada da Mai Maciji daga bangaren Kudu sai dai duk wasannin ba kisa.

’Yan kallo sun cika makil a fadar Sarkin Zazzau domin su cire kwarkwatar idanunsu tare da  taya Dan Isan Zazzau murnar haihuwar da Allah Ya ba shi kamar yadda jagoran ’yan wasan kuma mai masaukin baki, Anas Sadauki Dan Sarkin Fawa ya yi karin bayani. “Mun hadu ne domin taya dan uwanmu murnar samun karuwa ta haihuwa da Allah Ya ba shi, wato Dan Isan Zazzau. Mun taru ne saboda shi masoyin ’yan wasan damben gargajiya ne kuma duk wani abin arziki da ya faru a Masarautar Zazzau to muna ciki domin ita ce masarauta daya tilo a Arewa da take kokarin daga darajar wasan damben gargajiya wanda daya ne daga cikin al’adun da suka rage ga al’ummar Hausawa. Dalili na biyu kuma wadansu ba su taba ganin damben gargajiya ba, to ka ga a yau damben ya zo musu har gida,” inji shi.

Anas Sadauki ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi  su sa hannu wajen daga darajar wasan damben gargajiya ganin yadda yake samar wa matasa aikin yi.

Ya ce akalla ’yan wasa sama da 500 ne daga sassan kasar nan suka hadu a birnin Zariya, ban da ’yan kasuwa na wasu wurare da suka zo su suka baje kolinsu sannan suka bada tasu gudunmawa don inganta al’adunmu na gargajiya. Sarkin makadan ’yan damben Ashafa Ibrahim Dan Gulbi Zamfara  ya kayatar da ’yan kallo a filin wasan da kidan dambe.