✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi taho-mu-gama da masu zanga-zangar #EndSARS a Abuja

Wasu matasa dauke da muggan makamai sun afkawa masu zanga-zangar #EndSARS a Abuja

Wasu matasa dauke da muggan makamai sun yi arangama tsakaninsu da matasa masu zanga-zangar #EndSARS a Abuja.

Mutanen dai dauke da gorori da adduna da wukake sun far wa mutanen ranar Asabar suna tsaka da zanga-zangar.

Tun da farko dai matasan dake zanga-zangar sun yi tattaki a kan titin Gado Nasko dake cikin garin tun da misalin jarfe 7:30 har zuwa karfe 10 na safe.

Lamarin ya janyo cunkoson ababen hawa da ya hada da kananan motoci da kuma na dakon kaya.

Daga nan ne kuma wasu matasa da a ka bayyana a matsayin masu neman a dawo da SARS suka isa wajen dauke da makamai.

Lamarin dai na faruwa ne a lokacin da matasa masu zanga-zangar ke tikar rawa daga wakokin da su ka kunna a motocin da su ka yi amfani da su wajen killace hanyar, a yayin da a gefe guda kuma masu ababen hawa dake cigaba da taruwa ke cike da bakin ciki da fargaba.

Matasan da su ka kai farmakin sun nufi kan masu zanga-zangar yayinda da su kuma masu zanga-zangar suka cika wandonsu da iska sannan aka samu bude hanyar.

Gabanin hakan dai sai da ‘yan sanda suka yi yunkurin shawo kan masu zanga-zangar kan bude hanyar, amma lamarin ya ci tura.